Skip to main content

Posts

Featured

*KO RUWA NA GAMA BA KI*       *HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION* *Rubutawa: Hadiza Isyaku* *Sadaukarwa ga:- Sirrin 'ya mace group* *Wannan labari ƙirƙirarre ne, na yi shi don kawo gyara a cikin al'umma, ba don cin zarafin wani ko wata ba, Allah ya sa abin da ke ciki ya amfani Al-umma* *Godiya ga Allah S.W.A da Salati ga Baban Abdallah da Ibrahimul Mu'azzam Annabi Muhammad S.A.W* *Fatan Alkhairi ga ƴan ƙungiyata wato Hazaƙa writers, ina mana fatan Alkhairi da samun nasara bisa ga abin da muka sa gaba* *Shafi na ɗaya* "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Na shiga uku ni Asabe, wanne irin bala'i na ke gani haka a jikinki Jummai?".  Cikin tashin hankali Asabe ke faɗin haka lokacin da ta yi arba da matashin cikin da zai kai wata biyar zuwa shidda a jikin ɗiyarta Jummai, wanda tunda take ba ta taɓa lura da shi ba sai yau, sakamakon kodayaushe, Jumman na cikin hijabin da ta fa ke da sanyin da ake ne ya sa ta sanya shi. Jummai kuwa, da kullum ta ke f...

Latest posts

GABATARWA